
Dan majalisar dattawan Najeriya ya shawarci babban bankin Najeriya CBN, ya fara ware wasu kudade domin ciyarda yan Najeriya sakamakon yunwa da yan kasar ke fama da ita.
Jimoh Ibrahim ya ce akwai bukatar babban bankin kasar da ma'aikatar kudi su duba yiwuwar hakan domin ceto yan kasar daga tsananin yunwa da su ke fama da ita.
Dan majalisar dattawan wanda dan jam'iyya mai mulki ta APC daga jihar Ondo ya furta haka ne a birnin Washington DC, da ke kasar Amurka.
Jimoh ya ce, idan babban bankin ta karbi shawarar zai taimaka sosai wajen rage radadin talauci da yunwa da yan Najeriya ke ciki, duba da tsadar abubuwa da rashin darajar Naira.
Jimoh Ibrahim ya kara da cewa ya kamata ayi tsarin ta yadda zai taimakawa mutum miliyan 20 a kowani wata, har zuwa shekara guda.
Dan majalisar ya ce idan za a aiwatarda tallafin yadda talaka zai amfana kai tsaye ya fi alfanu maimakon bawa gwamnonin kasar su bawa talakawa.
Jimoh ya bayyana cewa idan kowani dan kasar mai shekaru daga 18 zuwa sama za a bashi tallafin Naira dubu 100 yadda mutum miliyon ashirin za su samu a kowani wata, cikin lokaci kadan kowani dan kasa zai farfado.
Dan majalisar ya ce, yin hakan ya fi ma'ana maimakon bada tallafin abinci da a lokuta da dama baya isa hannun wadanda ya kamata.
Jimoh Ibrahim ya ce, rashin tsarin taimakawa talakawan kasar mai nagarta shi ne ke kara tsananin talauci tsakanin yan Najeriya. Jimoh ya kara da cewa ya zama dole babban bankin Najeriya ta sake tunanin yadda za ta rika bawa yan kasar tallafi domin kawo karshen yunwa da yan kasar ke tattare da ita.