
Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya rantsarda zababbun shugabannin kananan hukumomi 44 a gidan gwamnati da ke birnin Kano.
An rantsarda shugabannin ne bayan sun lashe zabukan da aka gudanar a jihar ranar asabar, inda dukansu 'yan takaran jam'iyyar NNPP mai mulkin jihar Kano ne.
Daya daga cikin shugabannin kananan hukumomin 44 da su ka yi nasara mace ce, wacce ta lashe zaben karamar hukumar Tudun Wada.
Gwamna Abba ya bayyana muhimmancin zaben, inda ya ce kotun kolin Najeriya ce ta umarce gwamnonin kasar su gudanar da zaben kananan hukumomin.
Abba Kabir Yusuf ya ce, kotun kolin ta kuma umarci kowani gwamna a fadin kasar ya mikawa kananan hukumomin kudadensu kamar yadda gwamnatin tarayya ke tura musu.
Gwamna Abba ya ja hankalin shugabannin kananan hukumomin 44 da su bashi goyon baya ta hanyar gudanar da gwamnati mai adalci da rikon amana.
Abba Kabir ya kara da cewa gwamnatin sa ta na aikin tukuru don tabbatarda adalci ga kowani dan jihar Kano babba da yaro, mace da namiji.
Kwamishinan shari'a na jihar Haruna Isa Dederi ne ya rantsar da shugabannin 44 a wani biki da aka gudanar a gidan gwamnati da ke birnin Kano.
A nasa bangaren, shugaban hukumar zabe mai zaman kanta na jihar Kano Farfesa Sani Lawal Malunfashi, ya mikawa shugabannin 44 takardun lashe zabukan, inda ya ce, su ne su ka yi nasarar lashe zabukan kananan hukumomin da aka yi ranar asabar 26 ga wannan wata.
Akwai jam'iyoyi kamar AA da AAC da ADC da APM da Accord wadanda su ka yi takara da yan jam'iyyar NNPP a zaben kananan hukumomin amma ba su yi nasara ba.