
Dan takarar shugabancin Najeriya a zaben 2023 Peter Obi ya ce a shirye ya ke ya zama mataimakin shugaban kasa karkashin wata Jam'iyya idan aka bawa wanda ya dace.
Peter Obi ya bayyana cewa zai karbi tayin zaman mataimakin dan takarar shugaban kasa amma idan ya fahimci mutumin baida manufofin kawo ci gaba a kasa ba zai lamunta ba.
Obi ya ce ba lalle ne sai ya zama shugaban kasa ba, burin sa kawai shi ne Najeriya ta samu wanda zai fitar da ita daga halin da ta ke ciki.
Peter Obi ya ce har yanzu yana Jam'iyar sa ta Labour Party kuma ba zai lamunci wani kokari na amfani da shi ko Jam'iyar sa domin nasarar wani Wanda baya kishin al-umma ba.
Obi ya kara da cewa dole ne duk wanda yake so suyi tafiya tare, lalle ne ya bayyana mishi manufar sa na kawo canji musamman wajen kulawa da ilimin yara kanana da rashin gwamnati mai inganci ya hana su zuwa makaranta.